Isa ga babban shafi
Ukraine

EU ta nuna damurta kan rikicin birnin Kiev na Ukraine

Shugaban harkokin waje Kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini ta soki boren cikin wata sanarwa inda ta ke cewa abin takaici ne abin da ya faru.Yayin da Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko yace za a hukunta  wadanda ke da hannu wajen mummunar bore da aka yi a harabar majalisar kasar da ke birnin Kiev.

Rikicin Ukriane
Rikicin Ukriane
Talla

A  jawabin sa Poroshenko  ya yiwa mutan kasar bayyani cewa boren da aka yi ya sabawa dokokin kasar kuma za a sanya kafar wando daya da duk wadanda ke da hannu wajen kitsa boren da aiwatar da shi.

Yayin wannan bore dai wani jami'in tsaro na kasar, mai kimanin shekaru 24 ya rasa ransa, sannan kuma wasu mutanen sama da 100 sun samu raunuka.

Wannan bore na zuwa ne bayan da wakilan majalisar kasar suka zartas da amincewa da wata doka da ke goyon bayan matakin da ke bada karfin guiwa ga wasu yankuna Gwamnati da ‘yan tawaye ke rike da shi.

Shugaban kasar Russia Vladmir Putin ta bakin wani ma'aikacinsa ya soki abinda ya faru, amma kuma ya kara da cewa harka ce ta cikin gidan Ukraine.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.