kasashen Turai na taro kan tsaron jiragen kasar kasashensu daga yan Ta'adda
Ministocin cikin gida da sufurin kasasheTurai guda 9 , da suka hada da Fransa, Jamus, Britaniya, Itali , Spain, Beljiyom, Luxembourg, Holland da kuma kasar Suisse-land , a yau assabar sun soma wani taron a birnin Paris na kasar Faransa,
Wallafawa ranar:
zaman taron na yau dai ya ta'allaka ne a kan tattauna yadda kasashen za su karfafa matakan tsaron su a tashoshi da cikin jiragen kasar kasashen , bayan faruwar harin jirgin kasa na Thalys, dake karakaina tsakanin Amsterdam da Paris a makon da ya gabata.
Wannan al'amarin da ya kara tada hankalin kasashen turai dake fuskanatar barazana daga mayakan jihadi da yanzu haka suka bazu a nahiyar ta Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu