Isa ga babban shafi
Macedonia

Macedonia zata karbi Yan cirani

Kasar Macedonia ta sanar cewa za ta baiwa kadan daga cikin ‘Yan Cirani masauki duk da cewa ta rufe kan iyakarta da Girka saboda gududn kwarrar yan ciranin cikin Kasar.

Dubban Yan Cirani ne cikin wani hali bayan Macedonia ta hana su kutsa kai cikin kasar
Dubban Yan Cirani ne cikin wani hali bayan Macedonia ta hana su kutsa kai cikin kasar REUTERS/Ognen Teofilovski
Talla

Yanzu haka dubban yan ciranin ke cikin wani mawuyacin hali bayan hukumomin Macedonia sun dakile hanyarsu ta kutsawa cikin Kasar.

Ministan harkokin cikin gidan kasar ya ce daga cikin yan ciranin da zasu karba za su tallafa musu daidai gwargwado kuma hakan ma sai sun tattance mafi rauni daga cikin ‘yan ciranin kafin su amince.

Yanzu haka dai Yan cirani sama da dubu uku yawancinsu wadanda suka tserewa rikicin kasar Syria ne ke jibge akan iyakokin kasar Girka da Macedonia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.