Isa ga babban shafi
EU

Tarayyar Turai ta ware kudi domin magance matsalar ‘Yan ci-rani

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da matakin bai wa mambobinta kudi yuro biliyan 2.4 domin magance matsalar ‘Yan ci-rani da ke ci gaba da kwarara a kasashen.

Matsalar kwararan 'Yan ci-rani ta zama babbar barazana ga Turai
Matsalar kwararan 'Yan ci-rani ta zama babbar barazana ga Turai REUTERS/Guglielmo Mangiapane
Talla

Hukumomin Kungiyar sun bayyana cewa, kudaden za su taiwaka matuka ga kasashen da suka fi fama da matsalar Bakin-haure musamman kasashen Italiya da Girka da ke fuskantar matsalar bashi.

Kuma a makon daya gabata ne kasashen biyu suka ce ba za su iya gina wureren da su karbi bakin hauren ba.

Har ila yau, an tanadi wadannan kudaden domin kasashen Turai su inganta aikin sa ido a kan iyakokinsu tare da bunkasa shirye shiryen mayar da ‘yan ci-rani kasashen su na asali.

Mai Magana da yawun hukumar Nahiyar Turai, Natasha Bertaud ta shaidawa taron manema labarai cewa, yanzu sun samu damar bayar da makudan kudaden.

Jami’ar ta kara da cewa, suna kokaroin ganin an saki kudaden kan lokaci yayin da Italiya za ta karbi Yuro Miliyan 558, Girka kuma yuro miliyan 478.

A ranar juma’ar da ta gabata ne Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa bakin haure na fuskanatar mayuwacin hali a Girka yayin da Firaministan Kasar Alexis Tsipras ya bayyana cewa kasar ta kasa jurewa kwararar ‘yan ciranin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.