Faransa ta musanta cimma matsaya da Rasha kan cinikin jiragen Misrals
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya musanta cewa Kasarsa ta cimma yarjejeniyar karshe da Rasha kan cinikin jiragen ruwa na yaki samfurin Mistrals.
Wallafawa ranar:
Shugaba Hollande ya musanta sanarwar da Rasha ta fitar na cewa ta cimma matsayar karshe da Faransa bayan Faransan bata isar mata da jreragen yakin biyu ba duk da yarjejeniyar cinikin da suka fara kullawa a baya.
A cewar Hollande, ana ci gaba da tattaunawa da mahukuntan Faransa da Rasha kan wannnan batun kuma ya kara da cewa zai yanke shawara cikin yan makawanni masu zuwa.
Gaza cimma matsayar karshe kan Yarejejeniyar cinikin jiragen na mistrals mai daukan jirgi mai saukan ungulu, ta sa dankantarkar dake tsakanin kasashen biyu tsami sama da shekara guda, bayan hukumomin birnin Paris sun yanke shawarwar dakatar da yarjejeniyar siyar da jirgaren kan euro biliyan 1 da miliyan 200.
Kuma an dakartar da yarjejeniyar ne saboda takunkuman da kasashen yamma suka kakabawa kasar ta Rasha sakamakon mamaye yankin Crimea na Ukraine da Rashan ta yi, da kuma zargin da ake mata na baiwa 'yan arewan Ukraine goyon baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu