Isa ga babban shafi
Rasha

Shugaba Putin na Rasha ya bada umarnin lalata abinci da aka shigo dasu kasar

Shugaban Kasar Rasha, Vladmir Putin ya rattaba hannu kan wata doka da ta bada umarnin lalata kayayyakin abincin da aka shigo dasu kasar daga kasashen yamma bayan an haramta haka. 

Shugaban Kasar Rasha Vladmir Putin
Shugaban Kasar Rasha Vladmir Putin REUTERS/Alexander Nemenov/Pool
Talla

A shekarar data gabata ne hukumomin birnin Moscow suka hana shigo da abinci daga kasashen yamma domin mayar da martani dangane da takunkuman da aka kakaba wa Rasha saboda rikicin Ukraine.

 

Wannan dokar ta bada damar lalata kayayyakin abincin da aka shigo dasu ba tare da izini ba kuma a ranar 6 ga watan Agustan wannna shekarar ne za a lalata abincin.

An dai ga wadansu manyan motoci dauke da kayayyakin ciye-ciye na kokakrin kutsawa Rasha, inda aka dakatar dasu a kan iyakar kasar kuma har yanzu ana ci gaba da mayar da duk wani abinci da aka tsare wanda kuma ake kokarin shiga dashi kasar ta barauniyar hanya.

To sai dai wannan dokar bata bayyana karara ba, ko ana iya lalata wadannan kayayyakin abincin nan take a kan iyakar kasar da zaran an tsare su, ko kuma a’a yayin da kuma a ka bukaci gwamnati data sanar da tsarin da ya kamata a bi wajan lalatarwa.

A makon daya gaba ta ne Ministan albakatun gona na Rasha Alexader Tkachev ya gana da Shugaba Vladmir Putin in da ya bukaci jami’an kwastam da su lalata kayyakin abincin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.