Isa ga babban shafi
Faransa

Sama da Yan cirani dubu guda sun nemi shiga Ingila ta karkashin kasa

Akalla ‘Yan cirani 1,500 ne suka nemi tsallakawa zuwa Birtaniya daga Faransa ta hanyar karkashin kasa da ake bi zuwa kasashen Turai yayin da aka tabbatar da mutuwar mutun guda daga cikinsu.

Wasu daga cikin bakin hauren dake neman Manyan motocin dake bi ta hanyar karkashin kasar zuwa Ingila daga Faransa
Wasu daga cikin bakin hauren dake neman Manyan motocin dake bi ta hanyar karkashin kasar zuwa Ingila daga Faransa Reuters/路透社
Talla

Mutanen da suka yi kokarin shiga Kasar ta Ingila a jiya talata an tabbatar da mutuwarsa mutun daya daga cikinsu wanda dan asalin kasar Sudan ne.

Hanyar da jirgin kasa ke bi dauke da fasinjoji dai ta cunkushe a tsawon makwanni saboda yadda daruruwan ‘Yan ci raini ke kokarin hawa jiragen kasa da manyan motoci da ke bi ta hanyar zuwa Birtaniya daga Faransa.

Yanzu kuma mutane akalla 9 aka tabbatar da mutuwarsu tun a watan Yuni da ‘Yan ciranin suka gano hanyar ta zuwa Ingila.

Wannan kuma yasa yanzu ministocin Birtaniya da manyan jami’an tsaro zasu tattauna matsalar.

Yanzu haka hukumar Turai ta na shirin daukar matakan tsaro domin kare rayukan dubban ‘Yan ci rani da ke mutuwa a hanyar ta karkashin kasa domin shiga kasashen Turai.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.