Isa ga babban shafi
Japan

Dangin Dattijon Japan mai shekaru 102 sun shigar da kara kotu bayan ya kashe kansa

A Kasar Japan, Dangin Dattijan nan mai shekaru 102 da ya kashe kansa bayan an tirsasa masa kauracewa gidansa saboda yaduwar Nukliya, sun shigar da karar kamfanin TEPCO dake kula da masana’antar Nukliya ta Fukushima Kotu.

Mieko Sirikar Fumio Okubo dauke da hotansa
Mieko Sirikar Fumio Okubo dauke da hotansa japantimes.co.jp
Talla

Dattijan mai suna Fumio Okubo ya kashe kansa ne ta hanyar rataya bayan ya shiga halin damuwa saboda umarnin da gwamnatin Japan ta baiwa mazauna kauyan Litate mai tazarar kilomita 40 daga masana’antar ta Fukushima na ficewa daga gidajensu bayan ambaliyar ruwa ta tsunami ta lalata injinan dake sarrafa makamashin Nukliya na Fukushiman, lamarain da ya haifar da yaduwar Nukliyan wanda kuma ke matukar illa ga jama’a.

Okubo shine mazaunin da ya fi jimawa kauyan na Litate yayin da iyalansa suka bukaci kamfanin na TEPCO dake kula da harkokin masana’antar Fukushima da ya biya su diyyar Yen miliyan 60 wanda ya yi dai dai da Dalar Amurka dubu 485.

Wata sirikar Okubo mai suna Mieko ta shaidawa manema labarai cewa, suna bukatan ayi nazari kan yadda Dattijan da ya shafe tsawon shekaru 102 a duniya ya hallaka kansa lokaci guda, inda ta ce ya kamata a gane cewa ba karamar musiba ba ce zata sa shi yin haka.

A ranar 11 ga watan maris ne dai a shekara ta 2011 ambaliyar ruwa mai girman maki 9.0 ya hallaka kusan mutane dubu 18 a Japan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.