Isa ga babban shafi
Girka

Valery Giscard d’Estaing ya bukaci a dakatar da Girka daga cikin kasashen Turai

Tsohon Shugaban kasar Faransa da ya taimakawa kasar Girka ta shiga kungiyar kasashen Turai a shekarar 1981 Valery Giscard d’Estaing ya bukaci a dakatar da kasar daga cikin kungiyar tunda 'yan kasar sun ki amincewa da matsayin kungiyar.

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, Valery Giscard d’Estaing da Jacques Chirac
Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, Valery Giscard d’Estaing da Jacques Chirac AFP PHOTO POOL Charles Platiau
Talla

D’Estaing wanda ya jagoranci Faransa a shekarar 1974 da 1981 ya ce duk da ya ke baya nadamar sanya kasar cikin kungiyar da ke anfani da kudin euro, shugabanin ta na yanzu sun ci amanar kungiyar.

Wadanan kalamai na shi sun yi dai dai da na Tsohon Firaministan kasar Alain Juppe wanda ya ce ya dace a taimakawa Girka ficewa daga kungiyar.

Yau dai ake saran Shugabannin kasashen Turan za su gudanar da taron gagagwa a Brussels dan tattaunawa kan sakamakon zaben Girka da kuma shirin gwamnatin kasar na sake gabatar da wani sabon shirin bashin da kasar ke bukata.

Tattalin arzikin Girka dai cigaba da jin jiki ganin yadda Bankunan kasar ke rufe har sai jibi alhamis, da kuma karancin kudi a injinan daukar kudin ATM.

Kasashen Jamus da Faransa sun gabatar da matsayi guda inda suka bukaci Firaminista Alexi Tsipiras ya gabatar musu da sabon shirin kasar kan yadda za a taimaka mata da sabon bashi.

Sai dai Merkel ta ce har yanzu ba a samu yanayi mai kyau da za a baiwa Girka talafi ba saboda taurin bashin ta, saboda haka za su saurari abinda kasar za ta gabatar musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.