Isa ga babban shafi
Girka

Girka: Tsipras ya yi nasara a zaben raba gardama

Sama da kashi 61 na al’ummar Girka sun amince da bukatun Firaministan kasar Alexis Tsipras a zaben raba gardama da aka gudanar a karshen mako na yin watsi da matakan Tsuke bakin aljihun gwamnati da kungiyar Tarayyar turai da asusun lamuni suka gindaya wa kasar.

Firaminista Alexis Tsipras ya jinjinawa ‘'yan kasar Girka da suka amince da bukatunsa na yin watsi da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.
Firaminista Alexis Tsipras ya jinjinawa ‘'yan kasar Girka da suka amince da bukatunsa na yin watsi da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati. REUTERS
Talla

Hakan na nufin gwamnatin Girka ce ta samu nasara a zaben raba gardamar da aka gudanar a ranar Lahadi, sabanin masu bukatar shirin ceto tattalin arzikin kasar da Tarayyar Turai da kuma asusun lamuni na duniya IMF suka gabatar wa Girka.

Sama da kashi 61 na al’ummar Girka suka kada kuri’ar amincewa da bukatun gwamnatin Alexs Tsipras yayin da sama da kashi 38 suka kada kuri’ar amincewa da bukatun kasashen Turai da asusun lamuni na duniya da ke bin kasar bashi.

Sakamakon zaben raba gardamar dai ya nuna akwai alamun Girka na iya ficewa daga kungiyar kasashen Turai masu amfani da kudin euro.

A cikin jawabinsa Firaminista Alexis Tsipras ya jinjinawa ‘yan kasar da suka amince da bukatunsa na yin watsi da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati, yana mai cewa yanzu dama ce suka ba gwamnatin shi domin fito da hanyoyin magance matslolin Girka.

Yanzu haka kuma shugabannin kasashen Turai sun kira taron gaggawa kan batun Girka domin duba yadda za a bullo wa kasar bayan an ki amincewa da bukatunsu.

Girka dai ita ce kasa ta farko daga cikin kasashen da suka ci gaba da ta gaza biyan bashin da ake bin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.