Isa ga babban shafi
Girka-EU-IMF

Girka ta gaza biyan bashi

Kasar Girka ta dada fadawa cikin halin kunci sakamakon kasa biyan bashin da Hukumar bada lamuni ta duniya ke bin ta da ya kai euro biliyan guda da rabi, a yayin da wa’adin da aka dibar wa kasar ya kawo karshe a jiya Talata.

Girka za ta ci gaba da tattaunawa da ma su binta Bashi
Girka za ta ci gaba da tattaunawa da ma su binta Bashi REUTERS
Talla

Wannan mataki na kasar Girka ya sa ta zama kasa ta farko daga cikin kasashen da suk gaza biyan bashin hukumar bada lamuni ta duniya, ganin yadda duk wani kokari da kungiyar kasashen Turai ta yi na samun maslaha ya ci tura.

Kasa biyan bashin ya biyo bayan watanni biyar da aka shafe ana takun saka tsakanin Gwamnatin Girka da masu bin ta bashi wadanda ke ta kokarin ganin ba ta fice daga cikin kasashe masu anfani da kudin euro ba.

Ana sa ran ci gaba da tattaunawa yau Laraba bayan Girka ta sake neman wani lamunin shekaru biyu, wanda shi ne irinsa na uku a cikin shekaru biyar, yayin da kamfanonin da ke sa ido kan ci gaban tattalin arziki suka bayyana cewar kasar na gab da sake komawa cikin matsalar tattalin arziki a cikin wannan shekarar.

Hukumomin kasar sun yi alkawarin janye zaben raba gardamar da suka kira ranar Lahadi idan tattaunawar da za su yi a Brussels a yau Laraba ta amince da bukatun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.