Isa ga babban shafi
Girka-EU-IMF

Girka ba za ta biya bashin da ake bin ta akan lokaci ba

Gwamnatin kasar Girka ta ce ba za ta iya biyan wani kaso na bashin da Asusun Lamuni na Duniya ke binta ba kamar dai yadda aka shata a yau talata, yayin da wasu majiyoyi ke cewa kasar, ta gabatar wa kungiyar tarayyar Turai da wasu sabbin shawarwari kan yadda za a warware sabanin da ke tsakaninta da masu biyar ta bashi.

Tutar kasar Girka da kudin euro.
Tutar kasar Girka da kudin euro. Reuters
Talla

A yau talata ne dai wa’adin da kasashen duniya suka bai wa Girka na ta biya bashin da ake bin ta ko kuma a dakatar da bai wa kasar rance ke kawo karshe, to amma domin kaucewa haka, rahotanni daga birnin Athens na cewa gwamanati Alexis Tsipras ta gabatar da sabbin shawarwari kan yadda za'a ci gaba da hulda tsakanin kasar da wadannan cibiyoyi a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Kafin nan dai wata sanarwar daga ofishin Ministan kudin kasar, ta bayyana cewa Girka ba za ta biya wani kaso na kudaden da yawansu ya kai Euro bilyan daya da rabi ba da ya kamata ta zuba a wannan talata ba.

Hukumar kungiyar Tarayyar Turai kuwa ta sanar da bai wa firayi Minista Alexis karin sa’o’i 11 domin ya gaggauta karbar ka’idojin hukumar ko kuma a dauki matakin da ya dace a kan kasar, kuma idan har ya kasa mutunta wannan wa’adi, hakan na nufin cewa Girka ta zama kasar Turai ta farko da ta kasa cika sharadin a cikin shekaru 14 da suka gabata.

A ranar  lahadi mai zuwa ne dai za'a gudanar da zaben jin ra’ayin al’ummar kasar a game da karbar bashin ko kuma ficewa daga wannan tsari na kungiyar Tarayyar Turai da kuma asusun lamuni na IMF.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.