Isa ga babban shafi
Faransa

Maharin Faransa ya ce ba ya da wata alaka da addini

Mutumin da ya kai hari a wata cibiyar Gas inda ya fille kan maigidansa ya shaidawa ma su bincike cewa harin da ya kai ba ya da wata alaka da addini duk da an ji yana Kabbara a lokacin da ya kai harin. Wannan na zuwa ne a yayin ake danganta maharin da kungiyar Mayakan IS da ke da’awar Jihadi.

'Yan sandan Faransa sun cafke Yassin Salhi wanda ya kai hari a Lyon ranar Juma'a
'Yan sandan Faransa sun cafke Yassin Salhi wanda ya kai hari a Lyon ranar Juma'a REUTERS/Emmanuel Foudrot
Talla

Yassin Salhi mai shekaru 35 ya amsa laifin fille kan maigidansa da ya dauke shi aiki tare da rataye kansa a katanga a lokacin da ya kai hari a gabacin Faransa a ranar Juma’ar makon jiya.

Maharin ya ce harin da ya kai baya da nasaba da addini kamar yadda wasu ke kallon harin irin na mayakan da ke da’awar jihadi.

Sai dai kuma mata majiya da ke kusa da masu bincike tace maharin bai yi bayani akan Kabbarar da aka ji ya furta ba a lokacin da ya kai harin na ranar Juma’a a Faransa wanda ya raunana mutane da dama.

Rahotanni sun ce kafin kai harin maharin ya samu sabani da abokin aikinsa, al ‘amarin da ke nuna cewa harin baya da nasaba da tsautsauran ra’ayi. Amma masu bincike sun zanta da mahafiyar Salhi da kanwarsa, wadanda suka ce ya tafi kasar Syria a 2009, kafin barkewar rikici a kasar da kuma bullar mayakan IS.

Yanzu haka dai maharin ya shafe sa’o’i 72 a hannun ‘Yan sanda ba tare da an tuhume shi a kotu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.