Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta kara kasafin kudinta saboda ta'addanci

Dangane da barazanar ayyukan ta’addanci da take fuskanta, kasar Fransa ta bayyana shawarar kara yawan kasafin kudin tsaron kasar, da kusan biliyan 4 na Euro daga shekara ta 2016 zuwa 2019

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande
Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande REUTERS/路透社
Talla

Tun bayan hare haren ta’addancin watan janairun da aka kai a birnin Paris da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 17, Faransa ta kara jan damara domin tunkarar barazanar dake gabanta.

A lokacin da yake jawabi ga zaman taron majalisar tsaron kasar da ta hada manyan jami’an siyasa, da na sojan kasar , Shugaba François Hollande ya ce, Faransa ta daura damarar yaki da babbar barazanar hare haren ta’addanci a ciki da wajenta.

Hollande ya kara da cewa wannan ne yasa tun farkon wannan shekara ta 2015 dakarun soja dubu 10 dake aikin sintirin tsaro da nufin kare wurare masu muhimmanci na Faransa, za a kara yawansu da wasu sojojin dubu 7.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.