Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta karfafa matakan tsaro saboda ta'addaci a kasar

Gwamnatin Farnasa ta sanar da karfafa matakan tsaro bayan kama wani matashi dake neman kaddamar da hare hare a Kasar

Firaminstan Faransa, Manuel Valls
Firaminstan Faransa, Manuel Valls Reuters
Talla

Firaministan Kasar Manuel Valls ya bayyana cewa, a lokacin zaman taron ministoci a fadar Shugaban kasar, sun tattauna kan nasarar da jami’an tsaro suka yi na kama matashin wanda bicinken farko ya tabbatar cewa ya na shirin kai wasu hare hare a kasar.

Valls ya kara da cewa, kama matashin babbar nasara ce , kuma daukacin masu yaki da ta’adanci a kasar ta Faransa zasu kara kaimi a aikinsu domin zakulo duk wanda ke da hannu a wanan al’amari.

A bayanin Valls, ya tunatar da jama’a laifin da matashin ya aikata a baya, inda yace, ya na da hannu a kisan da aka yiwa matar nan mai suna Aurelie Chatelain, lamarin da ya bakanta wa gwamnatin Faransa rai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.