Isa ga babban shafi
Faransa-India

Indiya ta saye jiragen yakin Faransa

Firaministan kasar Indiya Narendra Modi da ke ziyara a kasar Faransa ya sanar da rattaba hannu a wata yarjejeniya tsakani kasarsa da Faransa kan cinikin wasu jiragen yaki samfarin Rafales Jet guda 36.

Firaministan India Narendra Modi tare da Shugaban Faransa Francois Hollande
Firaministan India Narendra Modi tare da Shugaban Faransa Francois Hollande REUTERS/Charles Platiau
Talla

Rahotanni sun ce India ta saye jiragen ne akan kudi da suka kai sama da dala Biliyan 4.

Dangantakar kasashen ta sake bai wa katafaren kamfani kera jirage na Faransa Dassault damar samun kudaden shiga bayan ganimar da kamfanin ya samu a watan Fabrairu da ya gabata inda ya sayar da jirage 24 ga kasar Masar.

Shugaban Faransa Francois Hollande da babbar murya ya bayyana cewa kasashen biyu za su ci gaba da hulda mai tasiri.

India na son mallakar jiragen ne domin kare barazanar kasashen Pakistan da China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.