Isa ga babban shafi
Faransa

Ma'aikatan Sa'ido a kan jiragen sama a Faransa sun shiga yajin aiki

Ma’aikatan dake aikin zura ido, ga zirga zirgar jiragen sama a Faransa, sun tsunduma cikin wani yajin aikin tsawon kwanaki 2, al’amarin da ya dagula harakokin sufurin jiragen sama a kasar ta Faransa  

Wani Jirgin Sama a sararin samaniya
Wani Jirgin Sama a sararin samaniya © Fotolia
Talla

Kungiyar ma’aikatan da ke kula da filayen sauka da tashin jiragen saman fararan hula ta Kasar Faransa ta ce, yajin aikin ya shafi ayyukan tashin kimanin kashi 40 cikin 100 na jiragen saman sufuri a kasar ta Faransa.

Ana ganin cewa, mai yiwuwa yajin aikin ya yi kamari sakamakon kiran da kungiyar ta yi na son ganin ‘ya ‘yanta sun gudanar da yajin aikin a ko ina cikin fadin kasar ta Fransa, domin bayyana takaicinta, kan matakan tsuke bakin aljihun da gwamnati ta dauka a wannan sashe nasu.

Babban Ofishin ma’aikatar dake kula da filayen jiragen saman farar hular ya bukaci kamfanonin jiragen saman kasar da su soke kimanin kashi 50 cikin 100 na tashi da saukan jirage a ranar alhamis.

A ranar laraba, Kamfanin jiragen saman nan mai saukin kudi na Easy Jet ya soke tashin jirage 118 a yayinda shi kuma na Ryan air, da yayi tir da matakin da ma’aikatan suka dauka ya soke tashin sama da jirage 250.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.