Hollande zai gabatar da jawabi ga taron Davos
Yau juma’a ana ci gaba da gudanar da taron tattalin arzikin duniya a birnin Davos na kasar Suisse, taron da ke samun halartar masana tattalin arziki da kuma masu fada-a-ji a siyasar duniya.
Wallafawa ranar:
A wannan juma’a shugaba Francois Hollande na Faransa zai gabatar da jawabi a gaban mahalarta taron sama da dubu biyu, kuma batun tattalin arziki musamman matsalolin kudi da Faransa da sauran kasashen Turai ke fama da su za su mamaye jawabin nasa.
Wasu daga cikin muhimman batutuwan da taron na Davos ke tattaunawa sun hada da sha’anin tsaro da kuma barazanar ta’addanci, yayin da faduwar farashin man fetur a duniya ke matsayin muhimmi ga mahalarta taron na bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu