Isa ga babban shafi
Ingila

Masarautar Buckingham ta Britaniya za ta cire lambobin yabonta

Masarautar Buckingham a kasar Britaniya ta ce za ta cire lambobin yabon da aka samu a farautar namun daji daga gidan tarihinta, saboda gudun kada kungiyar Tarrayar Turai da ke yaki da keta hakin dabbobi ta ci tararta bisa rashin dacewar ajiyar su.

greatlondon.ru
Talla

Fadar Buckingham ta sanar da kwashe kayyakin tarihin da suka kai 62 domin gudun karyar dokokin kungiyar Tarrayar Turain, ganin yawancinkayan ajiyar na dabbobi ne da ke fuskantar barazanar karewa daga doron kasa da kuma kungiyar ke yaki da farautarsu.

Daga cikin dabbobin da aka jera fatalensu a dakin tarihi da ke fadar, sun hada dana Zaki, da Damisa da Giwa da kuma na Giwan-ruwa wadanda masarautar ta samu sakamakon farautar da Sarakunan da suka yi mulki a kasar ta Britaniya suka yi shekaru aru aru da suka wuce.

Wannan mataki da masarautar ta dauka ya biyo bayan yunkurin da jikan Sarauniya Elizabeth Yarima William ya yi ne, inda yake gangamin na yaki da farauta ko yin barazana ga ire iren namun dajin da ake gudun karewarsu daga Duniya ganin hakan zai iya jan hankalin Tarrayar Turain.

Sai dai kuma yanzu haka akwai shakkun cewar Masarautar za ta kwashe wadanan Fatalen Dabbobin Dawan, kafin lokacin da za’a bude gidan tarihin domin ziyarar al’umma a watan Afrilu na shekara ta 2015.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.