Isa ga babban shafi
Austriya

Kungiyar OPEC ta ce ba za’a rage fitar da Man Fetir ba

Kungiyar kasashe masu samar da albarkatun Man Fetir ta Duniya OPEC, ta cimma matsayar daidaita yadda za ta ci gaba da samar da danyen Man a Duniya, duk da hasashen da aka yi na yiyuwar kasashen, su rage yawan fitar da albarkatun Man saboda faduwar farashinsa

blogs.wsj.com
Talla

Kamin soma gudanar da taron dai an yi hasashen cewar kungiyar za ta dauki matakin rage fitar da danyen man ne, lura da yadda farashinsa ke dada faduwa a Duniya kama daga Watan Yulin da ya gabata.

Yanzu dai kungiyar kasashen 12 sun amince da ci gaba da samar da Man na ganga miliyan 30 a Rana, matakin da ake akai har na tsawon shekaru 3 da suka gabata.

Sai dai an bayyana yanda kassahe matalauta daga cikin kassahen da ke samar da danyen Man Fetir din kamar Ecoudor da Venezuella suka kalubalanci masu kumbar susa daga cikinsu, kan wannan matakin da a nasu gani, ka iya kara tauye tattalin arzikinsu idan farashin Man na dada faduwa.

Matakin kin rage fitar da Man da kungiyar ta dauka dai ya kara tsawon lokacin da aka kwashe ana fama da wannan matsalar ta faduwar farashinsa, daga shekara 3 zuwa 4, kuma hakan, na illa ga kasashe ‘yan rabbana-ka-wadatamu, da kuma samar da karin riba ga kasashe masu sarrafa kayan masana’antu kamar su China da Amurka da dai sauransu.

Taron dai an gudanar da shi ne a Vienna inda mambobin kasashen 12 suka halarta tare da tattaunawa da kuma fitar da sakamakon bayan taron daga bisani.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.