Faransa: An fara tuhumar tsohon shugaba Sarkozy kan rashawa
Masu shigar da kara sun fara tuhumar tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, bisa zarginsa da ake yin a karbar wasu kudade ta haramtacciyar hanya.
Wallafawa ranar:
Tuhumar ta biyo bayan kwashe sa’oi 15 da da Sarkozy ya yi yana amsa tambayoyi a gaban ‘yan sanda, lamarin da ya zamanto na farko a kasar da aka tuhumi wani tsohon shugaban kasar.
A yau Laraba kuma an fara tuhumar Sarkozy inda zai bayyana a gaban alkali domin fara shari’a bisa wasu hujjoji da ake da su a kanshi.
Idan dai har aka samu Sarkozy da laifi a wannan tuhuma zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu