Isa ga babban shafi
Ukraine

Petro ya lashe zaben shugabancin kasar Ukraine

Sakamakon zaben shugabancin kasar Ukraine da aka gudanar a jiya lahadi, ya bayyana attajiri Petro Poroshenko a matsayin wanda ya yi nasara a wannan zabe.

Petro Porochenko, zababben shugaban Ukraine
Petro Porochenko, zababben shugaban Ukraine DR
Talla

Petro Poroshenko mai shekaru 48 a duniya ya lshe zaben na jiya da kusan kashi 56 cikin dari yayin da tsohuwar Firaiyi minista Yulia Tymoshenko ke biye masa da kusan kashi 13 cikin dari.

Sakamakon wannan tazara da ke tsakanin ‘yan takarar biyu, ya kawar da duk wata bukatar gudanar da zaben zagaye na biyu.

Al’ummar kasar sun fito da dama sun jefa kuri’arsu duk da cewa an sami baraka a wasu sassa sakamakon harin da magoya bayan Russia suka kai.

Poroshenko yayin jefa kuri’arsa, ya ce abu na farko da zai fi mayar da hankali bayan an zabe shi ne maido da zaman lafiya a kasar ya kuma kara da cewa nan ba da jimawa za mu kawar da cin hanci da rashawa da kuma gaggauta batun shigar kasar a kungiyar tarayyar Turai.

Poroshenko wanda attajiri ne a baya ya rike mukamin ministan harkokin waje tare da ministan cinikia da tattalin arziki a kasar ta Ukraine.

Ukraine na ci gaba da fafutukar ceto kanta bayan kutsen da Rasha ta yi na kwace yankin Crimea lamarin da ya jefa kasar cikin yakin da kawo yanzu ya janyo asarar rayukan mutane sama da 150.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.