Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine-Amurka

Matsayin kasashen duniya kan batun Crimea

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu ga Dokar da ta amince da Crimea a matsayin kasa mai cin gashin kanta, sakamakon kuri’ar raba-gardamar da mutanen yankin suka yi

Arseni Yatseniuk, shuaban riko na Ukraine
Arseni Yatseniuk, shuaban riko na Ukraine REUTERS/Alex Kuzmin
Talla

Sakamakon dai ya nuna yanda al’ummar yankin Cremea na kasar Ukraine suka jefa kuri’ar amincewa da hadewa da Rasha tare da ballewa Ukraine Uwargijiyarsu ta daa.

Sakamakon dai bai zo wa Amurka da sauran kasashen Turai da dadi ba, abinda ya kaisu ga daukar matakan kakabawa Rasha Takunkummai na karya tattalin arziki, amma a nata hauji Rasha ko a jikinta, domin shugaban kasar Vladimir Putin bai fito ya yi tsokaci akan matakin kasashen ba.

Kanfanin Dillancin labaran Russia ne ya ruwaito labarin wanda ya amince da garin Sevastopol a matsayin baban birnin Yantacciyar kasar Crimea.

Wannan dai shi ne mataki na karshe na fito-na-fito tsakanin Rasha da kasashen Yammcin Duniya.

Bisa daukar wannan matakin da Rasha ta yi, yanzu Cremea ta zamo ‘yantacciyar kasa mai cin gashin kanta sabanin yanda take a karkashin kasar Ukrain a inda aka fito.

Yanzu dai ba’a san irin matakin da kasar Amurka da kasashen kungiyar tarayyar Turai za su dauka ba, akan wannan batu, lura da yanda a cikin fushi suka kakabawa Rasha Takunkumi akan wannan batu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.