Isa ga babban shafi
Switzerland

An murkushe yunkurin fashin jirgin saman Ethiopian Airlines

Jami’an tsaro a kasar Switzerland sun samu nasara murkushe wani mutum da ya yi yunkurin fashin jirgin saman daukar fasinja mallakin kamfanin Ehiopian Airlines bayan da jirgin ya sauka a birnin Birnin Geneva.

Jirgin sama kirar Boeing 767 mallakin Canada
Jirgin sama kirar Boeing 767 mallakin Canada Wikimedias Commons/Adrian Pingstone
Talla

Jirgin dai ya taso ne daga birnin Adis Ababa na Habasha a kan hanyarsa ta zuwa Rome na Italia kafin a karkata akalarsa, kuma ‘yan sanda sun ce an cafke wanda ya yi yunkurin aikata fashin wanda shi ma ma’aikacin jirgin ne.

Jirgin kirar Boeing 767, ya baro birnin Adis Ababa ne da misalin karfe 12 da rabi na daren jiya, da nufin isa birnin Rome da misalin karfe 4 da minti 40 na safe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.