Isa ga babban shafi
Turai

An samu yawaitar ciniki ta Intanet a Turai

Wasu alkalumma a Turai sun ce an samu yawaitar ciniki ta saye da sayarwa ta hanyar Intanet a lokacin da ake hada hadar kasuwanci domin bikin Kirsemeti, amma a kasashen Faransa da Birtaniya ‘Yan kasuwa sun samu cikas saboda matsalar yanayi na iska mai karfi da ruwan sama da ya dakatar da harakoki da dama.

Wani bangare na sayar da kayan shafe shafe a Turai
Wani bangare na sayar da kayan shafe shafe a Turai
Talla

Kasuwannin Hannayen jarin Turai sun tashi sama Kafin lokacin da aka takaita hada hadar kasuwancin a jiya Talata saboda hutun Kirsemeti.

Alkalumman sun ce an samu raguwar masu shiga kasuwa ko shaguna da kashi sama da biyu tun a makon jiya inda mutane suka fi gudanar da mu’amalar cikini ta hanyar Intanet inda mutune ke yin odar abu ta hanyar intanet kuma a kawo masa har gida ba tare da sun leka kasuwa ba.

Farashin danyen mai kuma ya haura sama musamman saboda hutun kirsemeti da kuma rikicin Sudan ta kudu wacce tana daya daga cikin kasashen da ke fitar da danyen mai.

Tuni Ma’aikatar Fetir a Sudan ta kudu ta bayar da sanarwar dakatar da fitar da danyen mai a kasuwannin duniya.

Hakan ke nuna a kasuwar man ta duniya an yi hasarar ganganr mai 45,000 da Sudan ta kudu ke fitarwa duk a rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.