Isa ga babban shafi
Rasha

Hukumomin kasar Rasha sun yi afuwa ga Mikhail Khodorkovsky

A yau Juma’a shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya yi afuwa ga wani mutun da ya shafe shekaru 10 yana zaman kaso a kasar. Mikhail Khodorkovsky shine dan fusunan kasar ta Rasha da ya fi shahara, kuma sakin shi ya baiwa mutane da dama mamaki.Mikhail Khodorkovsky, ya rikito daga daga zama mutumin da ya fi kowa arzikmi a kasar ta Rasha, inda yake da dukiyar da ta kai Dalar Amurka Biliyon 15, ya zama fursuna, tsawon sheakru 10.Daure shi da hukumomin birnin Moscow suka yi, ya sake karfafa kallon hadrin kajin da kasashen duniya ke yi wa kasar kan zargin tauye hakkin dan adam.Magoya bayan shi na zargin cewa sau 2 ana daure shugaban katafaren kamfanin Mai na Yukos, kan laifukan da bai san hawa ba balle sauka, sakamakon bayar da tallafin kudi ga abokin adawar Putin, a farkon hazan shugaban mulki.Har yanzu ba wanda ya san rawar da Khodorkovsky zai taka a kasar, sai dai alamu na nuna cewa Shugaba Putin ba zai sako shi ba, in har yana ganin shi a matsayin wata barazana gare shi.Mahaifiyar Khodorkovsky, gyatuma mai shekaru 79 a duniya, da aka sako shi saboda rashin lafiyar ta, ta yi mamakin afuwar da shugaba Putin ya yi wa dan nata, kuma tace tana kokarin fahimtar abin da ke faruwa. 

Mikhail Khodorkovsky, lokacin da ya fito daga gidan yari
Mikhail Khodorkovsky, lokacin da ya fito daga gidan yari REUTERS/Sergei Karpukhin/Files
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.