Isa ga babban shafi
Ukraine

Kungiyar Turai ta katse kulla yarjejeniya da Ukraine

Kungiyar Tarayyar Turai ta dakatar da shirin kawancen da ta ke neman kullawa da kasar Ukraine ta kasuwanci sakamakon zanga-zanga da daruruwan mutanen kasar ke gudanarwa musamman ‘Yan adawa da ke kiran lalle sai gwamnatin Viktor Yanukovych ta kulla yarjejeniyar da Turai sabanin Rasha.

Daruruwan masu zanga-zangar goyon bayan kawancen kasuwanci da Kungiyar Tarayyar Turai a kasar Ukraine
Daruruwan masu zanga-zangar goyon bayan kawancen kasuwanci da Kungiyar Tarayyar Turai a kasar Ukraine REUTERS/Gleb Garanich
Talla

Daruruwan Masu Zanga-zanga ne suka fito domin ci gaba da zanga-zangar kin jinin gwamnati saboda kin amincewa da yarjejeniyar kasuwancin da Kungiyar Turai.

Kasar Ukraine mai yawan mutane Miliyan 46 wacce kuma tana cikin tsohuwar daular Soviet ta shiga rudani ne tun lokacin da gwamnatin Yanukovych ta yi watsi da yarjejeniyar kungiyar Tarayyar Turai inda shugaban ya gwammace ya kulla kawancen kasuwanci da Rasha.

Kungiyar Turai ta katse kawancen ne tsakaninta da Ukraine bayan da shugaba Yanukovych yaki rattaba hannu akan yarjejeniyar.

A gobe Talata ne ake sa ran shugaba Yanukovych zai kai ziyara kasar Rasha domin tattaunawa da shugaba Vladimir Putin duk da zanga-zangar adawa da ke ci gaba da kadawa a birnin Kiev.

‘Yan adawa dai sun shirya gudanar da wata babbar zanga-zanga domin karo da ziyarar da Yanukovych zai kai wa Putin yayin da Amurka ke bayyana goyon bayanta ga ‘Yan adawa a wata ziyara da Sanata John McCain ya kai a Ukraine.

Kungiyar Turai tace zasu iya ci gaba da tattaunawa amma dole sai idan Ukraine ta sa kanta ga shirin kulla yarjejeniyar. Yayin da gwamnatin Ukraine ta nemi rance kudi euro Biliyan 20 kafin ta amince da yarjejeniyar.

Sanata McCain ya gana da shugabannin adawa da suka hada Vitaly Klitschko, da jam’iyyar Tsohuwar Firaminista Yulia Tymoshenko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.