Isa ga babban shafi
Rasha

Putin ya nemi kungiyar tarayyar Turai da ta daina tsangwamar Ukraine

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bukaci Shugabannin kasashen Turai da su daina furta bakaken kalaman da su ke yi game da batun amincewar kasar Ukraine kan yarjejeniyar hadahadar kasuwanci.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Shugaba Vladimir Putin wanda yake magana bayan ya gana da Fira Ministan kasar Italiya Enrico Letta, ya ce shakka babu muddin kasar Ukraine ta rattaba hannu cikin wannan yarjejeniyar kasuwanci zai haifar da cikas ga harkokin kasuwancin Rasha

Ya kuma kara da cewa kasar Ukraine ya dace ta dauki matakin da ya dace, kuma Rasha za ta mutunta dukkan matsayin da Ukraine ta dauka.

A cewar Putin sha’anin aikin gona, ma’aikatun kera motoci da na jiragen sama za su shafu, muddin dai Ukraine ta kulla yarjejeniya da Kungiyar Turai, inda ya ce jaddada cewa Rasha ba za ta yarda ta bude kofarta ga kayayyakin kasashen Turai ba.

Kasar Ukraine inji, Putin na bin Rasha basukan da suka kaina kudi sama da Dala biliyan 30.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.