Isa ga babban shafi
Venezuela

An yi Jana'izar shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez

An dai fara gudanar da bukin binne Gawar marigayin shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ne da yammacin ranar Jumu'a. An dai bayyana halartar shugabannin kasashen yankin nahiyar Turai da Latin Amurka da Nahiyar Afruka ne, ta hanyar kiran Sunayen shugabannin kasashen dai bayan daya

Jama'izar shugaba Hugo Chavez a kasar Venezuela
Jama'izar shugaba Hugo Chavez a kasar Venezuela REUTERS/Miraflores Palace/Handout
Talla

Akalla dai an bayyana cewar shugabannin kasashe 35 ne suka halarci Jana'izar da kansu baya ga wadanda aka wakilta.

An dai bayyana cewar hakama ana gudanar da bukin rantsar da mataimakin sa Nicolas Maduro, kamar yanda tsarin kundin Doka na kasar ya tanadar.

Sai dai wasu Rahotanni na nuna cewar 'yan adawa sun kauracewa rantsar da mataimakin shugaban kasar suna masu bayyana rantsar dashi a matsayin abinda ya keta Doka.

Mataimakin shugaban jam'iyyar Democratic Union Roundtable DUR Angel Medina yace sam, Jam'iyyun adawa basu yarda da rantsar da mataimakin ba.

Daga cikin shugabannin kasashen da suka halarci Jana'izar sun hada da shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad wanda ya sha Tafi daga mahalartan Jana'izar, lokacin da aka kira sunan sa.

Wannan dai na nuna yadda kyakkyawar dangantaka take tsakanin kasar Iran da Venezuela wadda a lokacin mulkin shugaba Hugo Chavez bata da kyakkyawar dangantaka da kasar Amurka.

Kasar Amurka dai na dada nuna kwadayin gyara huldar ta da Venezuela bayan mutuwar Chavez, a karkashin sabuwar gwamnati mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.