Isa ga babban shafi
Bulgeria

Firaministan Bulgaria ya yi murabus tare da gwamnatinsa

Firaminsitan kasar Bulgaria ya yi murabus tare da gwamnatinsa domin amsa kiran ‘yan kasar da suka kwashe kwanaki suna zanga-zzanga. Wannan ne kuma ya bude kofar gudanar da sabon zabe a kasar. Firaminsitan kasar Boyko Borisov, ya ce ya yi murabus ne domin ba ‘Yan kasar ‘yancinsu da suka zabe su.  

Firaministan kasar Bulgaria, Boyko Borisov
Firaministan kasar Bulgaria, Boyko Borisov REUTERS/Julia Lazarova
Talla

“Bazan saka kaina a cikin gwamnatin da ‘yan sanda ke muzgunawa jama’a ba, ko kuma inda aka maye gurbin tattaunawa da barazana.” Inji Borisov.
 

A watan Aprilu mai zuwa ne ake sa ran za a gudanar da zabe, inda a yanzu haka Shugaban kasar zai zabi gwamnatin rikon kwarya domin tafiyar da harkokin kasar kamin zaben.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.