Isa ga babban shafi
Turai

An dage haramcin amfani da nama don ciyar da kifaye a Turai

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da dage haramcin yin amfani da naman aladu da  na tsuntsaye domin sarrafa abincin kifaye, haramcin da aka sanya sakamakon bullar cutar haukar shanu a cikin shekarun da suka gabata a nahiyar. A shekarar 1997 ne, kungiyar ta sanar da daukar matakin da ke haramta yin amfani da irin wannan nama a cikin gidajen kiwon dabbobi, kafin daga bisani a sanya haramci ga dukkanin masu kiwon dabbobi na kasuwanci ko kuma masu zaman kansu a shekarar 2001,Daukar mataki dai ya zone kwanaki kadan bayan da aka tabbatar da bullar cutar nan ta haukar shanu, da ta yi matukar tayar da hankulan jama’a a nahiyar ta Turai da ma sauran yankunan duniya.Alkaluma na baya-bayan nan da Hukumar kungiyar tarayyar Turai ta fitar, sun yi nuni da cewa ana samu gagarumar nasara a kokarin kawar da cutar ta haukar shanu, yayin da wani binciken da kwararru suka gudanar ya ce, ana iya samun yaduwar cutar daga shanu zuwa kananan dabbobi dangin awakai da raguna.Sakamakon sanya wannan takunkumi da aka yi, a shekarun da suka gabata, masu kiwon kifi a nahiyar sun rika yin amfani da naman kifi domin ciyar da sauran kifayensu, duk da cewa wannnan hanya ce mai matukar tsada ga masu gudanar da irin wannan sana’a. A ranar daya ga watan Yuni mai zuwa, ake sa ran kawo karshen wannan haramci baki dayansa. 

Wasu kifayen da ake kiwo
Wasu kifayen da ake kiwo Reuters/Srdjan Zivulovic
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.