Isa ga babban shafi
Birtaniya

Kasar Birtaniya ta ce bazata hana shiga da naman doki ba

Kasar Britaniya ta ce bazata hana shiga kasar da naman doki domin jama’a su ci ba, sai dai idan masana sun gano cewa akwai illar cin naman doki ga bil’adama. Ministan Abinci na kasar Britaniya, Owen Paterson ya ce bukatun a haramta shiga kasar da naman dawakai ba za ta sabu yanzu ba, amma dazaran jamian kiwon lafiya suka nuna cin naman doki nada illa ga mutun, ba za a yi wata-wata ba wajen hana ganinsa a cikin kasar. 

Firaministan Birtaniya, David Cameron
Firaministan Birtaniya, David Cameron REUTERS/Pascal Lauener
Talla

Cin naman doki dai a kasar Britaniya jama’a sun la’anci cin naman doki, to amma yanzu da asiri ya tonu aksarin wuraren sayar da kayan kwalama da ake sa nama ciki, kan kasancewar duk naman doki ake amfani da shi.

Tun gano wannan zance dai, ‘yan kasar Britaniya keta yin kira da a haramta shiga kasar da nama kowane iri.

A kasar Faransa ma shagunan sayar da nama, nata janye tsubin naman da suka ajiye da suke kyautata zaton da doki a ciki, kuma hukumomin Faransa sun kaddamar da binciken gano gaskiyar yaduwar wannan nama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.