Isa ga babban shafi
Faransa-Mali-Emirats

Shugaba Hollande na Faransa ya fara wata ziyara a Daular Larabawa

Shugaban kasar Fransa Francois Hollande ya ki janye ziyararsa zuwa kasar daular larabawa duk kuwa da suka yin haka da yake she a kasar a daidai lokacin da sojojin kasar ta Fransa ke yaki a kasar Mali 

shugaban kasar Faransa, Françcois Hollande
shugaban kasar Faransa, Françcois Hollande REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Majiyar fadar shugaban kasar ta Fransa ta bayyana cewa, shugaba hollande da a jiya litanin ya fara ziyarar tasa a daular ta larabawa daga can zai ci gaba da jagorantar yakin da dakarun Fransar ke tabkawa day an tawayen Islamar a kasar Mali.

Har ila yau a lokacin ziyarar a Abu Dabi Hollande zai gana da shugaban kasar Mauritaniya mai makwabtaka da kasar Mali wato Mohmed Ould Abdulaziz da ke ziyarar mako guda a yankin gabas ta tsakkiya

Muhimman batutuwan da zasu mamaye wannan ziyara ta Hollande a daular larabawa dai, sun hada ne da na tattalin arziki, tsaro da kuma makamashi, inda shuwagabannin kasashen 2 zasu tattauna ta fannin cinakin jiragen saman yaki da faransa ke kerawa samfarin Rafal, da kuma musaya ta fannin ta fanin danyen man petur da Allah ya horewa Daular ta Larabawa.

Sai dai kuma wannan ziyara ta Hollande na ci gaba da shan suka da daga yan adawa a Fransa wadanda ke ganin bai dace ba, ya kai wannan ziyara a daidai lokacin da kasar ta fara yaki a kasar Mali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.