Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 24/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 25/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 25/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 24/01 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 24/01 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 25/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 25/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 24/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 24/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 25/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 25/01 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 24/01 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 25/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 25/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 24/01 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 24/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 24/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

Ziyarata Algeria ba ta neman gafara ba ce, inji Hollande

media Shugaba Hollande tare da takwaransa Abdelaziz Bouteflika a ziyarar da ya kai kasar Algeria AFP PHOTO/BERTRAND LANGLOIS/POOL

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande yace ziyarar shi a Algeria ba ta neman gafarar laifukan da Faransa ta aikata ba ne a Algeria a zamanin mulkin mallaka kamar yadda wasu suka bukata. Amma Shugaban yace ziyarar ta bude sabuwar danganta tsakanin kasashen biyu.

“Ziyarata Algeria ba ta neman gafara ba ce illa na kawo ziyara ne domin yin abinda ya dace” inji Hollande yana shedawa manema labarai.

Sai dai Shugaban ya amsa laifukan kasar Faransa da ta aikata wa mutanen Algeria a zamanin mulkin mallaka.

Kafin dai ziyarar shugaban wasu ‘Jam’iyyun siyasa guda 10 hadi da jam'iyyar ‘Yan uwa Musulmi sun bukaci lalle sai Faransa ta nemi gafara tare da biyan diyyar laifukan da ta aikata shekaru 132 da suka gabata.

Hollande yace Ziyarar shi ta dole ce domin inganta hulda tsakanin kasashen Biyu ta fuskar tattalin arziki da tsaro.

Shugaba Hollande dai ya samu tarba ta musamman daga shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika bayan kwashe lokaci kasashen biyu na adawa da juna musamman a zamanin mulkin Nicolas Sarkozy.

Akwai dai Miliyoyan mutanen Algeria da ke zama a Faransa kuma wasu daruruwa daga cikinsu sun sauya sheka zuwa Faransawa.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure