Isa ga babban shafi
Rasha

An kaddamar da sabon samame akan ‘Yan adawan Rasha

An kaddamar sabon samame akan ‘Yan adawa da ake zargin sun yi kokarin ture Shugaba Vladimir Putin daga karagar mulki bayan taimakon da suka samu daga kasashen waje.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Sergei Karpukhin
Talla

Samamen an kaishi ne akan gidajen ‘Yan adawa, Taisiya Alexandrova Yuri Nabutovsky da kuma Anna Kornilova, inda aka kwace takardu da na’ura mai kwakwalwa, kamar yadda mai Magana da yawun kwamitin binciken kasar, Vladimir Markin ya fada a wata raubutacciyar sanarwa.

A cewar Markin an gano cewa, dukkanin wadanda aka kai samamen gidansu, sun halarci wani taron karawa juna ilimi a kasar Lithuana a wannan shekara, inda aka tattauna akan yadda ake ture shugaba daga mulki a fakaice, kamar yadda ya faru a Ukeraine da Georgia.

Wannan samame da aka kai ya fado a dai dai lokacin da ake bikin cika shekarar nuna kin jinin gwamnatin Putin, inda aka gudanar da zanga zanga farko a kasar dake sukan mulkinsa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.