Isa ga babban shafi
EU

Zanga zanga ta barke a Turai domin adawa da matakan tsuke aljihu

Ma’aikata a kasashen Tarayyar Turai sun kaddamar da zanga-zanga da yajin aiki domin adawa da matakan tsuke bakin aljuhun Gwamnati da matsalar rashin aikin yi da ke addabarsu. Ana ganin zanga-zangar da yajin aiki, za su fi tsanani ne a kasashen Spain da Portugal da Italiya.

Wata mata rike da Tutar kasar Girka a  harabar Majalisar kasar lokacin da suke zanga-zangar dawa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati
Wata mata rike da Tutar kasar Girka a harabar Majalisar kasar lokacin da suke zanga-zangar dawa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati
Talla

Kasashen da ma’aikata za su shiga yajin aikin sun hada da kasashen Spain da Girka da Portugal da Italiya inda kuma za’a gudanar da zanga-zanga a kasashen Belguim da Jamus da Faransa da Birtaniya da kuma wasu kasashen da ke gabacin Turai.

Al’ummomin yankunan kasashen Nahiyar Turai na ci gaba da harzuka akan matsalolin kangin Bashi da karyewar tattalin arzikin kasa da rashin aikin yi da yanzu haka suka yi kamari a yankunan kasashe masu amfani da kudin Euro.

Tuni dai aka samu barkewar tashin hankali tsakanin masu zanga-zanga da ‘yan sanda a kasar Girka da Italiya da kuma Spain inda masu zanga-zangar na ci gaba da la’antar shugabanninsu

Yanzu haka kamfanonin jiragen sama a wasu kasashen sun dakatar da jigila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.