Isa ga babban shafi
Birtaniya

BBC ta fada rikici bayan yada Rahoton zargin lalata da kananan yara

Wasu Manyan ma’aikatan kafar yada labaran BBC sun fuskanci matsin lambar sauka daga mukaminsu sanadiyar dambarwar da ta biyo bayan yada wani labari da ke zargin wani Dan siyasa yana lalata da kananan Yara.

Sabon Ginin kafar yada labaran BBC a London
Sabon Ginin kafar yada labaran BBC a London REUTERS/Luke MacGregor
Talla

Wannan matsalar ce ta lakume kujerar Darantan yada labarai, Helen Boaden, da mataimakinta Stephen Mitchell da Babban Daraktan tashar George Entwistle.

Yanzu haka kuma Daraktan rikon kwarya Tim Davie, ya yi alkawarin magance matsalar sakamakon rahoton da tashar talabijin ta Newsnight ta dauka kan cin zarafin yara kanana.

Wani bincike da aka gudanar bayan bullowar wannan dambarwa a BBC ya gano akwai gazawa a aikin jarida wajen yada labarai ba tare da bin diddigin labari ba.

Kafar yada labaran BBC dai ta yada wani labari ne a Telebijin wanda ya zargi wani tsohon dan Majalisa Alistair McAlpine da cewar ya ci zarafin kananan yara a Wales a shekarar 1970.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.