Isa ga babban shafi
Slovakia

Farashin kayayyaki ya ta shi a Slovakia

Farashin kayayyaki a kasar Slovakia sun yi tashin goron zabi daga maki 3.4 zuwa maki 3.6 a watan Yunin da ya gabata, kamar yadda wata kididdiga da ake fitarwa a duk wata 12 ta nuna.

Talla

Tashin goron zabin kamar yadda alkaluma su ka nuna ya faru ne dalilin tashin farashin kudade a fanin sufuri da ilmi da kiwon lafiya.

A duk wata, farashin kayayyakin na tashi da maki 0.2 musamman a watan Yuni a bangaren Ilmi da kayayyakin masarufi.
 

A watan Aprilu kuma kayayyakin sun ta shi da maki 0.1

Slovakia kasa ce mai yawan mutane miliyan 5.4 wacce kuma ta shiga cikin kungiyar kasashen Tarayyar Turai a shekarar 2004 ta kuma shiga cikin kasashen Turai masu amfani da kudin Euro a shekarar 2009.

A bara kasar ta bayyana cewa, ta samu cigaba da maki 3.3 a tattalin arzikinta bayan ta samu bunkasa a fanonin daban daban a shekarar 2010.
 

Kasar na kuma sa ran tattalin arzikinta zai karu da maki 2.5 a wannan shekarar ta hanyar motoci da ta kan kera ta kuma sayar ga kasashe irinsu Jamus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.