Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande da Sarkozy sun yi kafada a bukin tuna Yakin Duniya

Shugaba mai jiran gado a kasar faransa, Francois Hollande da shugaban kasar mai barin gado, Nicolas Sarkozy a jiya talata sun tsaya kafada da kafada a wani taron tunawa da yakin duniya na biyu kwana uku kacal bayan zaben da aka gudanar lahadin da ta gabata.

François Hollande tare da Nicolas Sarkoz a ranar 8 ga watan Mayu lokacin da ake bukin tuna yakin Duniya na Biyu a birnin Paris
François Hollande tare da Nicolas Sarkoz a ranar 8 ga watan Mayu lokacin da ake bukin tuna yakin Duniya na Biyu a birnin Paris Reuters
Talla

Wannan shi ne karon farko da shugabanin biyu su ka hadu bayan zaben da aka yi a ranar lahadin da ta gabata wanda, Hollande ya ka da Sarkozy.

Hollande wanda da za a rantsar a ranar 15 ga watan Mayu an nuna su tare da Sarkozy sun ajiye furanni a tare a wani waje da aka kebe a birnin Paris domin tunawa da ranar yakin duniya na biyu.

Fadar shugaban kasar Faransa dai ta aika wa Hollande takardar gayyata ne wajen taron wacce kuma ya amsa.

 A kasar faransa an kebe, takwas ga watan Mayun kowace shekara don tunawa da yakin duniya na biyu inda ake rufe makarantu da bankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.