Isa ga babban shafi
Faransa

Kalubalen Matsalar Tattalin arzikin Turai zai hanawa Hollande hutu

Kwanaki bayan samun nasarar shi a zaben shugaban kasar Faransa, François Hollande zai fuskanci jerin bukatun Faransawa kafin kama aiki a fadar shugaban kasa. Babban kalubalen da ke gaban sabon Shugaban shi ne daidaita matsalar tattalin arzikin Faransa.

Sabon Shugaban kasar Faransa François Hollande a tsakiya da  Eva Joly da Cécile Duflot, a lokacin da suke taya shi murna
Sabon Shugaban kasar Faransa François Hollande a tsakiya da Eva Joly da Cécile Duflot, a lokacin da suke taya shi murna REUTERS/Fred Dufour
Talla

François Hollande ya doke Nicolas Sarkozy a zaben shugaban kasa amma akwai babban aiki a gaban shi.

Faransa dai na fama da matsalar rashin aiki yi da bashi da ke ci gaba da karuwa wanda hakan ke nuna Hollande baya da wani hutu da zai more bayan samun nasarar doke Sarkozy.

Michel Sapin wani dan Jam’iyyar Gurguzu kuma tsohon Ministan Kudin Faransa yace Hollande ba ya da wani hutu a gaban shi domin Tattalin arzikin kasa yana cikin wani hali.

Tun fara yakin neman zaben shi, Mista Hollande ya sha alwashin kawo sauyi a Faransa amma akwai wasu matsaloli da zasu yi barazana ga cim ma wannan kudirin.

Matakan Tsuke bakin Aljihun Gwamnati

Da farko Hollande yace zai yi kokarin sabunta tsaren tsaren tattalin arzikin Turai da Sarkozy da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel suka tsara.

Hollande yace ba lalle sai an dogara da matakan tsuke bakin aljihu ba kafin a warware matsalar tattalin arzikin kasashen Turai.

Wanannan matakin ne kuma ya janyo masa farin jini ga Faransawa da ma kasashe da ke fuskantar kalubalen matsalar tattalin arziki.

Bayan lashe zaben Hollande nan take ne Angela Merkel ta nemi ganawa da shi domin tattauna yarjejeniyar da suka tsara tsakaninta da Sarkozy.

A ranar 15 ga watan Mayu ne ake sa ran Hollande zai kai ziyara birnin Berlin domin tattaunawa da Merkel.

Inganta Masana’antu

A yakin neman Zaben Hollande ya yi alkawalin inganta kananan masana’antun Faransa domin samar da ayyukan yi ga Faransawa.

Sai dai masana Tattalin arziki suna ganin wannan matakin na Hollande babban kalubale ne a gabansa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.