Isa ga babban shafi
Turai

Mutane sama da 300 sun mutu sanadiyar dussar kankara a Turai

Adadin mutanen da san yi da dussar kankara ya kashe a Turai, sun zarce 300 yanzu haka, abinda ya haifar da matsalar sufuri da zirga zirga a kasashen Poland da Ukrain da Serbia  da Italiya bayan kwashe tsawon mako daya.

Dussar kankara kwance a saman kasa a kasar Ukraine
Dussar kankara kwance a saman kasa a kasar Ukraine REUTERS/Yevgeny Volokin
Talla

Rahotanni sun ce, yawancin mutanen da suka mutu, wadanda basu da muhalli ne, da matafiya.

Yanzu haka a Ukraine da Serbia da Poland, sojoji da ‘Yan Sanda ne ke aikin gaggawa don taimakawa mutane sama da 70,000 da ke fuskantar barazanar sanyi, yayin da aka gargadi mutane su zauna a cikin gidajensu.

Mahukuntan kasar Faransa a jiya Lahadi sun tsamo wata gawar wani mutum wanda tsananin sanyi ya kashe wanda hakan ne kuma ya kara yawan mamatan da suka mutu zuwa 306.

Yanzu haka an fi samun mutuwa a kasashen Italiya da Poland da Ukraine.

A kasar Ukraine an samu mutuwar mutane 131 yawancin su wadanda basu da muhalli ne dake sintiri a saman titi tun fara samun aukuwar yanayin sanyin kwanaki tara da suka gabata.

Akalla mutane kimanin 1,800 ne ke kwance a gadon asibiti wasunsu kuma su 3,000 ke neman muhalli a kasar Ukraine.

Masana yanayi sun bayyana cewa matsalar dussar kankaran ta fara yaduwa wasu kasashen Turai da wasu kasashen Arewacin Afrika inda aka ruwaito mutuwar mutane 16 a kasar Algeria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.