Kotun Norway ta daure Mutane biyu da Laifin Ta'addanci
Wata kotu a Oslo na kasar Norway ta daure wasu mutane biyu yau, saboda shirin kai mummunar hari bama-bamai kan kamfanin buga jaridar Denmark mai suna Jyllands-Posten, wadda ta yi wasu munanan kalamai da zane da suka danganta da Manzo Annabi Muhammadu (SAW).
Wallafawa ranar:
Mutanen biyu Mikael Davud wanda aka daure na tsawon shekaru bakwai, sai kuma Shawan Sadel Saeed Bujak wanda aka daure na tsawon shekaru uku da rabi
Kotun ta ce ta gamsu cewa jaridar wadda ta buga munanan bayanan, a watan bakwai na 2010, mutanen biyu sun tsara babbaka ofishin jaridar sannan kuma su kashe marubucin kalaman sabon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu