Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta kama shugaban tsageran Hutu a Rwanda

Wata kotu a kasar Jamus ta bayyana kama wasu manyan ‘yan tsageran kasar Ruwanda guda biyu wadanda ta kama da laifukan yaki da kisan kiyashin al’umma a kasar Rwanda da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.A watan Nuwamba shekarar 2009 ne jami’an kasar Jamus suka cafke shugaban Jam’iyyar FDLR Ignace Murwanashyaka da mataimakinsa Straton Musoni da suka gudu zuwa kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo bayan kokarin kifar da gwamnatin Paul kagame wanda ya janyo rikicin kasar Rwanda a shekarar 1994.Katun kasar Ta Jamus ta daura alhakin kisan daruruwan mutane ga Jam’iyyar ta FDLR tsakanin shekarar 2008 da shekarar 2009 a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo tare da laifin yiwa daruruwan mata fyde da kuma cin zarafin kananan yara.Shugabanni da dama ne dai kotun ta zarga a kisan kiyashin rikicin kasar Rwanda inda aka kiyasta mutuwar mutane 800,000 mafi yawancinsu ‘yan kabilar TutsisSai dai kuma bayan cafke su Shugabannin sun musanta dukkanin zargin da ake masu na laifukan da suka aikata a kasar Demokradiyyar Congo. 

Shugaban Jam'iyyar  FDLR Ignace Murwanashyaka,
Shugaban Jam'iyyar FDLR Ignace Murwanashyaka, AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.