Isa ga babban shafi
Faransa

Kaji Kusan 5000 Sun Mutu Saboda Karan Jiragen Sama

‘Yan sandan kasar Faransa sun fara binciken musabbabin mutuwar garken wasu kaji 4,800 na wani gidan gona.Wannan al'amari, kamar yadda wasu bayanai ke nunawa, na biyo bayan gittawan da wasu jiragen saman yaki  biyu ne masu karar gaske  sukayi.Likitocin dabbobi da suka gudanar da binciken matattun kajin , sun fahinci cewa kajin nada rai kafin gittawan jiragen, to amma bayan wucewar su ne sai kajin suka firgice har suka mutu.Etienne Le Mehaute, wanda ya mallaki gidan gonan inda ake kiwon kajin, yace ba don masu kiwon kajin na kusa ba, da kuwa hasarar ta zarce haka.Yace shi da kansa tare da iyanlansa ne suka garzaya zuwa wajen da kajin suke bayan jiragen saman sun gitta, inda suka karas da abinda ya faru. 

Irin Kajin Faransa da suka mutu
Irin Kajin Faransa da suka mutu rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.