Isa ga babban shafi
Cannes

Bukin Fina Finai Na Cannes

A cigaba da gudanar da gasan nunin fina-finai na Cannes da akeyi a kasar Faransa fitattun ‘yan fim tun daga Russell Crowe zuwa kamar su Jennifer lopez sun tara kudaden da suka kai Dollan Amirka kusan Million  7 da zasu bayar domin agaji ga masu fama da cutar kanjamau da kuma mutanen kasar Haiti dake cikin matsala.Kudaden an tara su ne a wajen wani bukin dare da aka shirye wajen gasan nunin fina finan na Cannes, wanda wata cibiya dake binciken Cutar Tsida dake Amirka (American Foundation for AIDS Research) ta shirya.A bara an tara abin da yakai kudin Turai Euro kusan miliyan hudu.Bayan bukin cin abincin, wanda shine babban taron tara kudade domin yaki da cutar kanjamau cikin wannan shekaran, Crowe da mawakin nan Lionel Ritchie sun tara kudaden da suka kai Dalan Amirka dubu dari ga mutanen kasar Haiti dake cikin matsala.A yau Jumaa sai da 'yan sanda suka tarwatsa  taron masu bore  awajen gasan nunin fina finan alokacin da ake tantance wadanda zasu kalli  wani fim gameda yakin samun 'yancin kasar Algeriya. 

Alamar Nunin Fina finan Cannes
Alamar Nunin Fina finan Cannes rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.