Shirin Kasuwa a kai miki Dole na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan yadda kasashen Turai ke ci gaba da kokarin zuba jari a kasashen Afrika a dai dai lokacin da China ta yi wa nahiyar kamun-kazan-kuku. Ko a baya bayan Theresa May ta Birtaniya da Angela Merkel sun ziyarci nahiyar, in da kowacce daga cikinsu ta halarci Najeriya ganin muhimmancin kasar a Afrika ta fuskar kasuwanci.
Sauran kashi-kashi
-
Yadda matsin rayuwa ya tilastawa 'yan Najeriya fasa rumbunan abinci
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yada zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya yi dubi kan matsanancin kuncin rayuwar da al’umman kasar suka shiga da har ta kai ana fasa rumbunan abinci ko tare manyan motocin dakon kaya a tituna ana kwasan abinci.06/03/202410:22 -
Faduwar darajar Naira ta tsayar da harkokin 'yan canji a makwaftan Najeriya
Shirin 'Kasuwa a kai miki dole' na wannan mako ya tattauna akan yadda faduwar darajar Naira ke haddasa koma bayan kasuwar 'yan canji a makwaftan Najeriya.07/02/202410:19 -
Dalilan soke lasisin wasu kamfanonin wutar lantarki
Shirin Kasuwa a Kai Maki Dole na wannan mako, ya mayar da hankali ne a game da batun wutar lantarki a Najeriya, bangaren da ke fama da matsalololi tsawon shekaru.Shirin zai yi dubi ne a game da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na sokewa da kuma sabunta lasisi ga wasu kamfanonin da ke da alhaki rarraba wuta a cikin kasar.31/01/202410:02 -
Yadda faduwar darajar Naira ke yin illa ga kasuwanci a Najeriya
Shirin 'Kasuwa a kai miki dole' na wanna makon ya mayar da hankali akan faduwar darajar naira da ke ci gaba da yin illa ga harkokin kasuwanci a sassan Najeriya.24/01/202409:52 -
Yadda rufe iyakar Benin ya haifar da tsadar rayuwa a Nijar
Shirin "Kasuwa akai Miki dole" na wanan mako tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Dosso dake Jamhuriya Nijar, yankin da ke kan iyaka da birnin Cotonou na Jamhuriya Benin inda jama'a suka shiga matsanancin halin tsadar rayuwa tare da kariyar tattalin arziki, sakamakon takun-kuman da Kungiyayoyi irinsu ECOWAS ko CEDEAO suka laftawa kasar, saboda Juyin mulkin da Sojoji sukayi.22/11/202309:50