Isa ga babban shafi
Kasuwanci

Kasuwannin hannayen jari na duniya sun girgiza

Kasuwanin hannayen jarin manyan kasashen duniya sun girgiza matuka a ranar Litinin tare da haddasa shakku a zukatan masu saka jari.

Rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China sun yi tasiri kan kasuwannin hannayen jari na manyan kasashen duniya
Rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China sun yi tasiri kan kasuwannin hannayen jari na manyan kasashen duniya Reuters/路透社
Talla

Manyan kasuwannin hannayen jari a yankin Turai, wato Frankfurt da kuma Paris, dukkaninsu sun fuskanci koma-baya, to sai dai takwararsu ta birnin London ta dan samu habaka a ranar Litinin.

A can kuwa Wall Street da ke Amurka, kasuwar Dow Jones da ke New York, rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China ne ke ci gaba da yin tasiri, tare da hana kasuwar samun daidaito a cewar masanin tsarin tattalin arziki, Charles Schwab.A

Alkaluman da aka fitar na nuni da cewa kasuwannin yankin Asiya sun fara mirmijewa daga tasirin rikicin kasuwancin na Amurka da China, yayin da takardar kudin Yuan na China ta fara farfadowa daga koma-bayan da ta fuskanta a ‘yan kwanakin da suka gabata.

A tsawon watan Yulin da ya gabata ne, kasuwannin hannayen jarin suka fi fuskantar yanayi na tangal-tangal sakamakon rikicin kasuwancin da ke tsakanin manyan kasashen na duniya guda biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.