Isa ga babban shafi
Turai

Tarayyar Turai za ta bankado kamfanonin da basa biyan haraji

Ministocin kudi na kasashen kungiyar tarayyar turai EU suna tattaunawa kan yadda za su aiwatar da shirin samar da kundin sunayen manyan kamfanonin nahiyar da ke kauracewa biyan haraji. Matakin na zuwa bayan bankado asirin inda manyan attajiran duniya da kamfanoni ke boye kadarori ko dukiyarsu, dan kin biya musu haraji.

Shugaban kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk.
Shugaban kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk. REUTERS/Yves Herman
Talla

Sama da shekara guda kenan gwamnatocin kasashe 28 da ke karkashin kungiyar ta EU ke tattaunawa don tsara yadda za su samar da wannan kundi na tattara sunayen manyan kamfanoni da attijaran nahiyar da suka boye wani yanki na tarin dunkiyarsu a kasashen turan da basu da dokoki masu tsauri kan biyan haraji.

Daga cikin irin wadannan kasashe akwai Ireland, Malta da kuma Luxembourg.

Binciken baya bayan nan ya nuna cewa hatta kamfanin Apple ya boye dukiyar sa mai tarin yawa daga Ireland zuwa tsibirin Jersey da ke daf da Faransa, bayan tsaurara dokoki kan biyan haraji da gwamnatin Ireland din ta yi.

Zalika ta bayyana cewa kasar Luxemburg ta dagewa kamfanoni da dama biyan haraji, alokacin da shugaban kungiyar EU mai ci Jean Claude Juncker ya ke Fira Minista.

Kan haka ne kungiyar tarayyar turan ta gargadi akalla kasashe 60 kan dole su gyara dokokinsu kan biyan haraji kafin nan da ranar 18 ga wanna wata, domin kaucewa suma a shigar da su cikin waccan kundi na masu kauracewa biyan harajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.