Isa ga babban shafi
IMF

Rage kudaden ruwa zai tsananta tattalin arziki -IMF

Wani rahoton Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya bayyana cewa, tsarin rage kudaden ruwa na dogon lokaci zai tsananta kalubalen tattalin arziki da duniya ke fuskanta, musamman idan bankuna da kamfanonin hada-hadar kudade suka ci gaba da aiki da tsarin.

Shugaban Hukumar bada lamuni ta duniya, IMF, Christine largarde.
Shugaban Hukumar bada lamuni ta duniya, IMF, Christine largarde.
Talla

Asusun bada lamuni na duniya ya bayyana haka a wani shirinsa na bitar halin da kasuwannin hada-hadar kudaden duniya ke ciki a duk bayan shekaru biyu-biyu, kuma hakan na zuwa ne a yayin da baitil malin Amurka ke shirin kara kayyadajjen farashin kudin ruwa.

Amurkan dai na son a yi amfani da sabon kayadajjen farashi ne a cikin watanni shidan karshe na wannan shekara ta 2017.

Sai dai har yanzu, farashin kudin ruwa na da rahusar da ba a taba ganin irinta ba a tarihin Amurka, amma farashin ya fi sauki a sauran manyan bankunan kashen diuniya.

Rahoton na IMF ya ce, daukan tsawon lokaci akan tsarin rage farashin kudin ruwa zai haifar da kalubale ga cibiyoyin hada-hadar kudade.

Matukar dai aka ci gaba da haka, bankuna za su gamu da hasara a kudaden shigarsu, yayin da kamfanonin Inshora za su tsincin kansu a cikin tsaka mai wuya.

Sannan kuma kananan bankuna za su bukaci hadewa da juna don gudun durkushewa ko kuma samun sauki.

Kazalika tsarin zai kawo jinkiri dangane da habbakar tattalin arzikin kasashe da kuma koma-baya wajen samar da kayayyaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.