Hotunan zaben Shugabancin Liberia

Jami’an zabe a Liberia su na ci gaba da kidayar kuri’un da ‘yan kasar suka kada a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu da ya gudana a ranar Talata, inda aka fafata tsakanin tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Sanata George Weah, da kuma mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai.

Tsohuwar Shugabar Kosovo Atifete Jahjaga a zantawarta da wakilin RFI Hausa kan Zaben Liberia a birnin Monrovia

Jagoran Cibiyar bunkasa Dimokradiya ta NDI kuma tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na sanya ido kan yadda ake kidaya kuri'u a Monrovia

Tsohon shugaban Najeriya kuma jogoran tawagar NDI Goodluck Jonathan yayin zantawa da manema labarai a Liberia

Daya daga cikin Jami'an Cibiyar bunkasa Dimokradiya ta NDI Christopher Fomunyo na tattaunawa da Wakilin RFI Hausa

Wasu daga cikin Jami'an hukumar zaben Liberia

Jami'an hukumar zabe na kidaya kuri'u har a cikin dare

'Yan Liberia sun kasa kunen suna bibiyan sakamakon zaben ta akwatin Redio

Wasu daga cikin magoya bayan George Weah na dakon sakamakon zaben

Magoya bayan George Weah na murna nasara tun kafin a fito da sakamakon zabe

Dan takara Joseph Nyuma Boakai na Jam'iyyar UP a lokacin zantawa da manema labarai

Jami'an kwantar da tarzoma na sintiri a gaban ofishin hukumar zabe

Jami'an kwantar da tarzoma sun tsaurara tsaro a birnin Monrovia